Asabar 19 Satumba 2026 - 20:48
Boyayyen Sirrin Kasancewar Amurka a Gabashin Siriya: Daga Satar Mai Zuwa Amfani da Ragowar Ɗaliban ISIS

Hauza/ Wani jami’in tsaron Siriya ya bayyana dabarun da Amurka ke amfani da su wajen kwace albarkatun mai da kuma katse hanyoyin tallafawa Ƙungiyoyin Gwagwarmaya (Axis of Resistance).

A cewar rahoton Sashen Fassara na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, wani jami’in tsaron Siriya ya bayyana wasu bayanai game da dabarun da sojojin mamayar Amurka ke amfani da su wajen ci gaba da kasancewa a cikin ƙasar Siriya. Ya jaddada cewa, duk da ikirarin janye sojojinta ƙarƙashin abin da ake kira “Ƙawancen Ƙasashen Duniya”, Washington tana bin wata manufa ta rarraba sojoji a wurare daban-daban da sake tura su, domin rage kuɗaɗen gudanar da ayyukanta da kuma tabbatar da iko a kan muhimman yankuna, da nufin cimma shirye-shiryen mamaya da rinjaye.

Jami’in ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da shafin Al-Malouma, inda ya ce sojojin mamayar Amurka sun dogara ne da wani tsarin sansanonin soja masu sauƙin sauyawa, wanda ya ƙunshi kusan sojojin Amurka 2,500. An rarraba waɗannan sojoji a yankunan arewa maso gabashin Siriya, musamman a lardunan Hasakah, Deir ez-Zor da Raqqa. Suna kuma da sansanoni a muhimman wurare kamar Kharab al-Jir, filin mai na Al-Omar da sansanin Al-Shaddadi.

Jami’in ya bayyana cewa, babbar manufar tura wannan sojoji ita ce ci gaba da satar mai da albarkatun da ke ƙarƙashin ƙasa, raunana ƙarfin al’ummar Siriya, tare da samar da kariya da mafaka ga ƙungiyoyin ta’addanci.

Sansanin Al-Tanf da Katse Hanyoyin Gwagwarmaya

Jami’in na Siriya ya ƙara da cewa, sansanin Al-Tanf, wanda yake a kan iyakar ƙasashen Siriya, Iraki da Jordan, kuma ya kai zurfin kilomita 55, shi ne ginshiƙin shirin Amurka na raba iyakoki da katse hanyoyin tallafawa Ƙungiyoyin Gwagwarmaya.

Ya bayyana cewa, mamayar Amurka ta kafa wasu sansanoni na ɓoye da kuma madadin sansanoni, waɗanda suke aiki bisa tsarin motsi cikin sauri. Haka kuma, ana daidaita ayyukansu da wasu wurare a yankin, kamar Al-Burj 22 da ke Jordan, domin gudanar da leƙen asirin na’ura mai kwakwalwa, gargadin farko da kuma sa ido kan iyakokin Iran da Iraki.

Ƙoƙarin Katse Hanyar Tehran–Baghdad–Damascus–Beirut

Jami’in ya bayyana cewa, ƙoƙarin Amurka ya fi mayar da hankali ne kan rufe muhimmiyar hanyar ƙasa ta Tehran–Baghdad–Dimashƙ–Beirut, wadda ke haɗa sojojin Ƙungiyar Gwagwarmaya da juna.

Ya kuma ce, Amurka tana amfani da ragowar ƴan ƙungiyar ISIS tare da gudanar da ayyukansu, sannan tana ƙoƙarin kawar da wasu kwamandoji waɗanda suka ƙi miƙa wuya ga muradun Amurka, ta hanyar kisan gilla da ake shirya wa.

Amfani da Ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya a Matsayin Rufin Baya

Jami’in ya bayyana cewa, Washington tana hulɗa da wata hukuma a Dimashƙa da ta kafa ta hanyar tilasta wani sabon yanayi a ƙasa, ba tare da bin wasu ƙudurran ƙasa da ƙasa ba, ciki har da Ƙuduri na 2254.

A cewarsa, ana amfani da wannan ƙuduri a matsayin rufin baya domin tallafa wa ayyukan da ke nufin raba ƙasar Siriya.

Sansanonin Amurka Sun Zama Abubuwan Kai Wa Hari

Jami’in tsaron ya ci gaba da cewa, babbar matsalar Amurka ita ce, sansanonin mamayarta sun zama wuraren da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai suke kai hare-hare akai-akai.

Saboda haka, Washington ta koma amfani da wasu kamfanonin tsaro masu zaman kansu na ƙasashe daban-daban, waɗanda suke ɗauke da ma’aikata tsakanin 500 zuwa 900, ƙarƙashin sa ido kai tsaye na sojojin Amurka.

Ya ce, hakan na taimaka wa Amurka wajen kauce wa saka sojojinta kai tsaye cikin ayyuka masu hatsari, kamar kisan gilla da satar albarkatu.

Wasu daga cikin waɗannan ma’aikatan tsaro suna samun horo na dabarun jigilar kayayyaki da sauran ayyukan tallafi a Iraki. Manufar hakan ita ce tabbatar da ci gaba da kasancewar Amurka a yankin da ƙaramin kuɗi, tare da hana gwamnatin Siriya da kawayenta sake karɓe ikon yankunan gabashin ƙasar.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha